User:HausaDictionary/Hadiths

From Wiktionary
Jump to navigation Jump to search

Translate, combine, verify the English and Hausa 40 Hadiths into a single page[1].

# Hadisin a Hausa The Hadith in English
1 Hadisi na Ɗaya

An Karɓo daga hannun Sarkin Musulmi Abu Hafsi Umaru ɗan Haɗɗabi (Yardar Allah ta tabbata a gare shi), yace: Na ji Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yana cewa,

"Ayyuka da niyyoyi su ke tafiya kurum, kuma cewa abin da mutum ya yi niyya kaɗai, shi ya kan samu. To, wanda hijirarsa ta zama sabo da Allah da kuma Ma'aikinsa ne, to, sakamakon hijirarsa yana ga Allah da Ma'aikinsa. Wanda hijirarsa kuma ta zamanto don kwaɗayin samun duniya ne, ko kuma don mace ne da ya ke son ya aure ta, to, hijirarsa na ga abin nan da yayi ƙaura sabo da shi". 

Shugabannin masu ruwaito hadisai, Abu Abdul-lahi Muhammadu ɗan Isma'ila, ɗan Ibrahim, ɗan Mugiratu, ɗan Bardizbah, (Albuhari) mutumin Buhaira, da kuma Abul Husaini Muhammadu ɗan Hajjaji, ɗan Muslimu Al Kuhsairiyyu An-Naisaburiyyu, su suka ruwaito wannan hadisi a cikin ingantattun littattafan nan guda biyu, waɗanda su ke su ne mafiya ingancin littattafan hadisai da aka tsara.


On the authority of Omar bin Al-Khattab, who said : I heared the messenger of Allah salla Allah u alihi wa sallam say:

"Actions are but by intention and every man shall have but that which he intended. Thus he whose migration was for Allah and His messenger, his migration was for Allah and His messenger, and he whose migration was to achieve some worldly benefit or to take some woman in marriage, his migration was for that for which he migrated." 

related by Bukhari and Muslim.